27-Dec-2025
25-Dec-2025
24-Dec-2025
24-Dec-2025
21-Dec-2025
18-Dec-2025
17-Dec-2025
16-Dec-2025
29-Dec-2025
Shirin Duniyarmu A Yau na wannan karon, ya duba muhimman dabarun da kasar Sin ta sa gaba da yadda take kara kalailaice su domin tsara matakan ci gaban tattalin arzikinta da zamantakewa a cikin shekaru 5 masu zuwa. A farkon makon nan, firaministan kasar Li Qiang ya jaddada muhimmancin kara tace daftarin shirin bunkasa ci gaban kasa da kyautata zamantakewar al’umma na shekaru biyar-biyar karo na 15, wanda zai jagoranci manyan al'amurra da manufofin kasar a shekaru biyar masu zuwa. Wannan shirin na da nufin karfafa samar da ci gaba mai inganci, da karfafa kirkire-kirkire, da inganta tsarin tattalin arziki baki daya, da tabbatar da ci gaba mai dorewa da kyautata jin dadin jama'a.
24-Dec-2025
Tun fara kasuwancinta a asirce a wani tsohon gidan kwana dake lardin Jiangxi na kudu maso gabashin kasar Sin, har zuwa lokacin da ta zama jagora a sana'ar samar da hidimomi ga masu gidaje, inda ta jagoranci fiye da mata 2000 suka samu ayyukan yi, kokarin Luo Jia na tafiyar da kasuwanci na tsawon shekaru goma, bai haifar da wani gagarumin ci gaba ba a fagen fasaha, amma ya samar da wata hanya mai kyau ga mata ta asali, ta sauya matsayinsu daga “uwar gida” zuwa kwararriyar mai aiki”. Girmanta ya nuna yadda miliyoyin mata na kasar Sin suke neman ci gabansu ta kwarewarsu, da ma canza zaman rayuwsarsu ta hanyar aikin tukuru.
22-Dec-2025
22-Dec-2025