09-Nov-2025
08-Nov-2025
06-Nov-2025
05-Nov-2025
20251109-Yamai
00:00
1x
Yankin Daxing na birnin Beijing, ya dade yana more lakabin yankin kankana na kasar Sin. A yankin, akwai manoman kankana masu yawa. Wang Lili, manomiya a kauyen Zhaojiachang na yankin Daxing, ta karbe ragamar kula da harkokin kamfanin hada kan manoma don samar da sayar da kankana na Chunhua a 2018. Kuma tun daga sannan, Wang ke ci gaba da yayata amfani da sabbin fasahohi da fadada hanyoyin tallata kankana da gabatar da sabbin nau’o’in kankana. Yanzu ita ce babbar manajan kamfanin Chunhua, kuma mamba ce ta reshen kwamitin majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin a yankin Daxing. Haka kuma an ayyana ta a mastayin abar koyi a Beijing a 2023, kuma mai jagorantar mata ‘yan kasuwa a Beijing a shekarar 2024.
A cikin kungurmin daji ko yankin hamada dake kasar Kamaru, ana iya samun allunan tattara hasken rana da dama wadanda suke haskaka rayuwar mutane. A halin yanzu, wadannan alluna da ke bazuwa sosai a kasashen Afirka, suna tattara hasken rana da kuma mayar da shi zuwa karfin wutar lantarki, al’amarin da ba bayar da gudummawa ga sauya tsarin makamashi mai kiyaye muhalli na Afirka kawai yake yi ba, har ma yana canza rayuwa da makomar mazauna yankin sosai.
Domin habaka kiyaye al’adu masu dimbin tarihi ba kawai ga magada ba, har ma ga duniya baki daya bisa la’akari da shekaru aru-aru na wayewar kanta, kasar Masar ta bude babban gidan kayan tarihi na kasar, har ma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika wa shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi wani muhimmin sako mai tsuma zuciya na taya murna, da kuma jaddada muhimmancin kiyayewa da alfahari da tsoffin al'adun gargajiya da aka gada.
07-Nov-2025
03-Nov-2025
30-Oct-2025
12-Oct-2025
02-Nov-2025