20240922-Yamai
Kasar Sin ta janyo hankalin dimbin al’ummun kasashen waje domin gudanar da yawon shakatawa A shirinmu na yau, za mu mai da hankali ne kan aikin yawon shakatawa a kasar Sin. An ce a farkon rabin shekarar bana, yawan al’ummun kasashen waje da suka shigo kasar Sin ya kai miliyan 14 da dubu 635, adadin da ya karu da kaso 152.7% bisa na shekarar bara. Wannan batu ya nuna yadda kasar Sin ke janyo hankalin karin mutane masu yawon shakatawa na kasashe daban daban.