Sabuntawa Nan TakeDakika 10Dakika 30Sabuntawa Bisa Bin MatakaiSabuntawaKariSin na maraba da ’yan jaridar duniya da su halarci bikin cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin kin harin Japan da na tafarkin murdiyaZa a gudanar da bikin cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin kin harin Japan da Sinawa suka yi da yakin kin tafarkin murdiya da al’ummun duniya suka samu a nan birnin Beijing. Kuma Sin na maraba da zuwan ’yan jaridar kasa da kasa don su labarta wannan muhimmin lokaci. Dadin dadawa, Sin ta bude shafin yanar gizo mai adireshin http://kzjn80reg.zgjx.cn don saukaka yin rajista ga ’yan jaridar duniya da na yankunan Hongkong da Macao na Sin, kuma tana gayyatar ’yan jaridar da su yi rajista ta wannan hanya bisa gaggarumar maraba. Za a iya yin rajista ne daga raneku 15 zuwa 29 ga watan nan da muke ciki. Ban da wannan kuma, Sin za ta kafa cibiyar yada labarai yayin bikin ta yadda ’yan jarida na gida da na waje za su tafiyar da aikinsu cikin sawaba. Cibiyar za ta sauke nauyin dake wuyanta na maraba da ’yan jarida da gabatar da tarukan manema labarai daban-daban da ba da jagoranci ga aikin neman labarai da kuma kafa shafin yanar gizo na cibiyar da na WeChat, ta yadda za a yi amfani da fasahar intanet don baiwa ’yan jaridar hidimomi. (Amina Xu)Sauran LabaruXi Jinping ya gana da Kim Jong Un04-Sep-2025Nijeriya: An hallaka fiye da 'yan ta'adda 15 a wani hari ta sama04-Sep-2025Akalla mutane 29 ne suka mutu sakamakon kifewar kwale-kwale a yankin tsakiyar Nijeriya04-Sep-2025An yi wa Lai Ching-te na Taiwan rubdugu bisa kalamansa kan bikin tunawa da nasarar kasar Sin04-Sep-2025Kan sarki na musamman don tunawa da cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan da yakin duniya na kin tafarkin murdiya04-Sep-2025Sin ta wanzar da ruhin juriya ta hanyar yakar tafarkin murdiya04-Sep-2025Sana’ar manhaja ta karu a tsakanin watan Janairu zuwa na Yulin bana a Sin04-Sep-2025Hadarin kwale-kwale ya hallaka mutane 60 a jihar Naija ta yankin tsakiyar Najeriya04-Sep-202520250904-Yamai04-Sep-2025Xi ya gana da shugaban Zimbabwe da na jamhuriyar Kongo04-Sep-2025