A wani yanayi na kafuwar tarihi da zai wuce fadin dakunan wasanni, dan wasan kwallon tebur ta Snooker daga kasar Sin Zhao Xintong, ya shiga kundin tarihin wasanni na duniya, inda ya zama dan asalin kasar Sin na farko, kuma mutum na farko daga nahiyar Asiya da ya lashe kofin duniya na gasar kwallon Snooker.
15-May-2025
Ga dukkan alamu kara-kaina da tayar da jijiyoyin wuya da kumfar baki da suka turnuke harkokin cinikayya da tattalin arziki tsakanin giwayen duniya biyu ta fuskar karfin tattalin arziki, Sin da Amurka, sun kusa zuwa intaha, a yayin da taron kolin da sassan biyu suka yi a birnin Geneva na kasar Switzerland ya bude wani sabon babi tare da zama muhimmin mataki na dinke barakar da ta kunno kai a tsakaninsu game da kakabe-kakaben harajin kwastam.
14-May-2025
Kiemou Amadou, dan jarida ne daga Nijar da ke aiki da gidan radiyo da talabijin na Dounia a birnin Yamai. Kwanan nan, bisa goron gayyatar da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice ya aike masa, Kiemou Amadou tare da wani abokin aikinsa suka kawo ziyarar aiki kasar Sin. A shirin Sin da Afirka na makon da ya gabata, an gabatar da kashin farko na hirar da Murtala Zhang ya yi da malam Kiemou, inda ya bayyana wurare daban-daban da ya ziyarta a kasar Sin, tare da yin tsokaci kan abubuwan da suka burge shi...
13-May-2025