06-Oct-2025
06-Oct-2025
15-Sep-2025
09-Sep-2025
09-Sep-2025
19-Aug-2025
19-Aug-2025
04-Aug-2025
A matsayin wata muhimmiyar shawarar da kasar Sin ta baiwa duniya a sabon zamani, an kirkiro shawarar tsarin shugabancin duniya ne daidai lokacin da kasashe daban-daban ke kara samun iko da karfi. Tun bayan da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar a gun taron “kungiyar hadin-kai ta Shanghai wato SCO+”, a ranar 1 ga watan Satumbar bana, har zuwa yanzu, shawarar ta jawo hankalin bangarori daban daban na duniya, musamman ma kasashen Afirka. A cikin shirinmu na yau, zan yi muku bayani game da ra’ayoyin kwararrun kasashen Afirka kan shawarar tsarin shugabancin duniya.
08-Oct-2025
A ’yan kwanakin baya ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga makarantun horar da ’ya’yan JKS, da su kara azamar horar da dalibansu, ta yadda za su zamo masu kaifin basirar sauke nauyin dake wuyansu, kana makarantun su zamo cibiyoyin bayar da shawarwari ga JKS. Tun daga lokacin babban taron JKS na 18 da ya gudana a shekarar 2012, makarantun horar da ’yan jam’iyya a matakai daban daban ke ci gaba da daga matsayin ayyukansu na koyarwa da bincike, inda suke samun sabbin nasarori a ayyukansu.
08-Oct-2025
Abubakar Idris Muhammad Gwagwarwa, dan Kano ne wanda a yanzu haka yake karatun digiri na uku a bangaren kimiyyar lissafi wato mathematics a turance a jami’ar Central South University dake birnin Changsha na lardin Hunan na kasar Sin. A zantawarsa da Murtala Zhang, malam Abubakar Muhammad ya bayyana bambancin yanayin karatu tsakanin Najeriya da kasar Sin, da ra’ayinsa kan ci gaban kasar, gami da halayen mutanen kasar da suke matukar burge shi...
07-Oct-2025
Idan ka shiga kamfanin raya ayyukan gona na Qihong a lardin Jiangsu dake gabashin kasar Sin, to kyawawan kifaye nau’i Koi ne za su fara yi maka maraba. Kifayen na da matukar kyan gani. Guo Jun, babbar manajan kamfanin, ta shafe shekaru 10 na aikinta, wajen gina cikakken tsarin masana’anta na kiwo da sayarwa da raya harkar samar da kifin. Ta jagoranci mazauna garinsu wajen samun wadata na bai daya, ta hanyar inganta bunkasuwa da raya harkokin kauyenta.
06-Oct-2025