17-Sep-2025
15-Sep-2025
14-Sep-2025
Sannu a hankali, kasar Sin na ta nunawa duniya aniyarta ta aiwatar da matakai a zahiri, tare da ingiza matakan tabbatar da duniya ta hau turbar shugabanci bisa bin doka da adalci. Yayin da duniya ke fuskantar sabbin matsaloli na rashin jituwa nan-da-can, tsarin shugabancin duniya ma na fuskantar sabbin kalubale. Shi ya sa ma a yayin taron kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai, ko SCO da aka kammala a kwanan baya a nan Sin, shugaban kasar Xi Jinping ya gabatar da shawarar tsarin shugabancin duniya ko GGI, wadda ta tanadi karfafa bukatar himmatuwa wajen kare dokokin kasa da kasa.
17-Sep-2025
Kwanan nan ne, aka yi bikin matasan kasar Sin da kasashen Afirka karo na 9, inda wakilan matasan Afirka gami da wasu ’yan asalin Afirka dake zaune a sauran nahiyoyi suka hadu a nan kasar Sin, don kara fahimtar al’adun gargajiyar kasar, gami da nasarorin da kasar ta samu a fannonin raya yankunan karkara, da kiyaye muhallin halittu, da bunkasa sabbin fasahohi da sauransu. Mahamadou Djingarey, dan jarida ne daga babban gidan radiyo da talabijin na Jamhuriyar Nijar wato RTN, wanda ya kasance daya daga cikin bakin da aka gayyata zuwa kasar Sin don halartar ayyukan bikin matasan Sin da Afirka a wannan karo...
16-Sep-2025
Kauyen LeXiang da ke gundumar Rongjiang na lardin Guizhou a kudu maso yammacin kasar Sin, yanzu haka yana samun wani sabon kuzari saboda wasu matasan da suka dawo gida don gudanar da kasuwancinsu. Wadanda ke tsayawa kan gudanar da wasu ayyuka da suka shafi samar da ilmi ta hanyar tafiye-tafiye, da raya masana’antar yawon bude ido ta al’adu, wadanda kuma suka taimaka wajen ci gaban sana’ar otal masu zaman kansu. A cikin shekara daya kacal, kauyen ya samu masu bude ido sama da dubu 30. Karkashin hakan, wata cibiyar samun ilmi ta hanyar tafiye-tafiye da yarinya 'yar Guizhou mai suna Yang Xiangni ta kafa, tana karfafa tasiri sakamakon karbuwar da fim din nan na "Nezha 2" ya samu a kasar Sin. Wannan ‘yar kasuwa kuma wadda ke mayar da hankali kan yada wakar kabilar Dong, a yanzu haka tana jagorantar wasu yan mata wajen rubuta wani sabon labari game da kirkire-kirkire a fannin al’adun gargajiya.
15-Sep-2025
15-Sep-2025