Shirin bunkasa ci gaban tattalin arziki da zamantakewar jama’a na shekaru biyar-biyar da gwamnatin kasar Sin take aiwatarwa ya zama wani muhimmin ginshiki na mazaya kasar zuwa tudun-mun-tsira da samun nasarorin da suka zama gagara-badau a duniya ta fuskar ci gaban kasa. Da yake a kulli-yaumin kasar Sin na mayar da hankali kacokan game da yin waiwaye adon tafiya ga duk wasu al’amura na sha’anin shugabanci da gudanarwa domin tayar da komada a sassan dake bukatar hakan, Shugaban kasar Xi Jinping ya nanata batun daukar kwakkwaran mataki da ya amsa sunansa a dimokuradiyance, a karkashin doka wajen tabbatar da cewa an inganta shirin na bunkasa tattalin arziki da zamantakewa na shekaru biyar-biyar na gaba a matakin koli.
21-May-2025
A cikin ’yan shekarun da suka gabata, mu’amalar sada zumunta tsakanin Sin da Afirka ta habaka zuwa hadin gwiwar moriyar juna, wadda ta kawo sauyi ga rayuwar miliyoyin jama’a a nahiyar Afirka yadda ya kamata. A cikin shirinmu na yau, bari mu ji ra’ayin Yu Dunhai, jakadan kasar Sin a Najeriya, don kara fahimtar yanayin ci gaban kasashen Sin da Najeriya, da makomar hadin-gwiwarsu a nan gaba.
20-May-2025
A makon da ya wuce, mun gabatar muku wata mace mai suna Aotegenghua, ’yar kabilar Mongoliya, wadda ta ajiye aikinta na akanta, har ta fara aiki na dasa bishiyoyi a yankin hamada mai fadin hekta sama da dubu 2 a kasar Sin. A cikin shirinmu na yau, za mu ci gaba da kawo muku labari ne game da wannan baiwar Allah.
19-May-2025
19-May-2025