21-Mar-2025
20-Mar-2025
19-Mar-2025
18-Mar-2025
20250320-Yamai
00:00
1x
Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin JKS ko kuma CPC ta kaddamar da gangamin ilmantarwa a fadin jam'iyyar don aiwatar da shawarar "Mataki takwas" da manyan shugabanninta suka dauka domin kyautata halaye da dabi’u wajen gudanar da ayyuka. Gangamin wanda aka kaddamar bayan manyan tarukan kasa biyu na shekara-shekara na manyan 'yan majalisa da na masu ba da shawarwari kan harkokin siyasa wanda aka kammala a makon da ya gabata, zai ci gaba da gudana har zuwa karshen watan Yuli, kamar yadda wata babbar sanarwar da aka fitar a duk fadin jam'iyyar ta ayyana.
Abdulrazaq Yahuza Jere, sabon ma’aikaci ne na sashin Hausa na CMG, wato babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, wanda ya kasance babban edita a sashin Hausa na jaridar Leadership dake Abuja, Najeriya. Malam Abdulrazaq Yahuza Jere ya zanta da Murtala Zhang, inda ya bayyana dalilan da suka sa ya zo aiki kasar Sin, da kuma fahimtarsa game da ci gaban kasar...
A kowace rana da safe, dubban mutanen kasar Vietnam masu dauke da manya da kanana jakunkuna suna taruwa a titin Mong Cai da ke Vietnam don shiga kasar Sin, inda gagarumin shirinsu ke zama sabon abun kallo a bakin iyakar Dongxing dake tsakanin kasashen biyu. Daga cikin wadannan ma'aikatan da suke ketare iyaka don yin aiki, akwai ma'aikatan gidan kofi, da masu jagoroncin yawon shakatawa, wasu kuma suna yin cinikin kananan kayayyaki a Dongxing. A cikin shirin mu na yau, za mu kawo muku labari game da wata baiwar Allah, wadda ta kasance daya daga cikinsu, mai suna Wu Shi Qingxin, ’yar kasar Vietnam.
17-Mar-2025
06-Mar-2025
16-Mar-2025
15-Mar-2025